Kalli Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti wanda ya janyo cece-kuce

Advertisements


Wasu ma’aurata ‘yan Najeriya da har yanzu ba a gane ko su waye ba sun karade kafar sada zumunta da salon da suka bayyana yayin bikinsu.

A wani bidiyo da @iam_steveola ya wallafa, an ga yadda ake ruwan kudi a wani biki da nairori amma ake kwashewa da wata katuwar bokitin roba.

Bidiyon ya nuna zukekiyar amaryar sanye da kayan gargajiya tana zaune yayin da take kallon wasu maza biyu suna kwashe kudin a bokitin roba.

Kalli Bidiyon Qasa:

Is this foolishness or enjoyment??? pic.twitter.com/iLya0v8ppF

— Steven and 14 Others (@iam_steveola) March 23, 2021
Har yanzu dai ba a san lokaci ko wurin da aka yi bikin ba. Bidiyon tuni ya samu sama da tsokaci dubu takwas daga ma’abota amfani da Twitter.

Yayin da wasu ke mamakin yawan kudin da aka lika, wasu na nuna mamakinsu ne akan yadda ake kwashe kudin a bokitin roba.

DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

Advertisements

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like