Za’ayi Mummunar Ambaliyar Ruwan Sama A shekarar Bana – Inji Hukuma Duba Dalilinta

Advertisements


A ranar Laraba, 24 ga watan Maris, 2021, hukumar NIHSA da ke lura da sha’anin ruwa na kasa, ta bayyana cewa za a gamu da ambaliya a shekarar nan.

NIHSA ta yi kira ga gwamnatocin Najeriya sus tashi-tsaye, su shirya wa ambaliyar da ke tafe. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis.

Darekta Janar na hukumar NIHSA, Clement Nze, ya bada wannan sanarwa maras dadi a lokacin da ya kira taron manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Clement Nze yake cewa ambaliyar da za ayi za ta addabi jihohin Najeriya ne saboda a nan ne duk ruwan da ya taso daga sauran kasashen Afrika tara ya tsaya.

“Har yanzu akwai lokaci da jihohi da kananan hukumomi da sauran daidaikun mutane za su iya daukar matakan da za kare wannan musibar annoba a bana.”

Ruwan da ya taso daga Benin, Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Cote D’Ivoire, Guinea, Mall, da Niijar duk ya tike ne a kogin Najeriya, wanda hakan ke jawo ambaliya.

NIHSA ta bada shawarar a rika gina hanyoyin ruwa, a gyara kwatoci da bola. Haka zalika an bukaci mutane su cire ciyayi da tarkance da ke hanyoyin ruwa.

Mista Clement Nze, ya ke cewa ambaliya ta zama ruwan dare a Najeriya tun shekarar 2012 lokacin da aka gamu da babbar musibar da ba a taba ganin irin ta ba A cewar Nze, an yi asarar rayukan daruruwan mutane da kayan bilyoyi, sannan mutane da-dama sun koma ba su da matsuguni a sakamakon wannan ambaliya.

A bara idan za ku tuna, hukumar bada agaji na gaggawa na kasa watau NEMA ta ce za ayi ambaliyar ruwan sama a kananan hukumomi 102 da ke jihohi 28.

A jawabin da Daraktan ya gabatar, ya ce sun yi hasashen wannan ne sakamakon rahoton da ma’aikatar lura da karkokin ruwa a Najeriya, NIHSA ta fitar.

Advertisements

DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like