Yaron Jonathan ya yabi Tinubu, ya fadi sirrin doke jigon APC a 2023, ya ce zai yi kyau da mulki

Advertisements


Tsohon mukarrabin Goodluck Jonathan, Doyin Okupe, ya ce ‘yan siyasa Kudu maso yamma ne kadai za su iya samun nasara a kan Asiwaju Bola Tinubu. Dr. Doyin Okupe ya ce idan har tsohon gwaman na Legas ya fito takarar shugaban kasa, babu wadanda za su iya doke shi illa ‘yan siyasar kasar Yarbawa.

Doyin Okupe wanda ya yi aiki da Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan a fadar shugaban kasa ya na sha’awar neman takarar shugaban kasa a 2023.

Da ya ke wasu bayanai a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 28 ga watan Maris, 2021, Doyin Okupe ya tabbatar da cewa Bola Tinubu abin fargaba ne a zabe. Duk da karfin fitaccen jigon na APC a kudancin Najeriya, Okupe ya ce zai iya samun galaba a kansa.

But Bola Tinubu is coming in from a wrong party where he has such powerful antagonists that have capacity to stop him. D flagrant excesses of his party 2 which he never reacted publicly especially wt issues concerning d SW has made him not 2 be favoured by some of his own people.

— Doyin (@doyinokupe) March 28, 2021
“Na yi imani na kere masa kadan; na fi shi sanin siyasar kasa da takarar shugaban kasa, wajen tara masu kwakwalwa, za mu zo daya, idan ban na sha gabansa ba.” “A bangarena, zan yi masa lahani saboda ni kadai ne ke Bayaranen da ke neman shugaban kasa a PDP.”

“Bayan wannan, ina ganin cewa Tinubu abokin gaba ne mai ban tsoron gwabza wa a zaben 2003. Tinubu ya na cikin ‘yan siyasar da su ka fi kowa a zamanin nan.” “Dabararsa da sanin aiki, abin a yaba ne, a takaice, Tinubu zai dace da Shugaban kasa.” Inji Okupe.

Dr. Okupe ya ce matsalar da Tinubu zai samu shi ne ba ya magana kan batun Yarbawa, sannan akwai ‘yan jam’iyyarsa da ya taimaka da ke neman ganin bayansa. Ku na da labari cewa tun kafin a kai ko ina, an samu sabani a tsakanin manyan PDP game da yankin da za a ba takara a zaben shugaban kasa da za ayi a 2023.

Watakila PDP ta yi fatali da tsarin kama-kama da ake yi tsakanin Arewa da Kudu, musamman idan ta yi amfani da shawarar kwamitin Gwamna Bala Mohammed.

SOURCE: LEGIT.NG

 DAGA BZ NEWS 24/7

Advertisements

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like