Da duminsa: An Sake Cinnawa Sufetan ‘Yan Sanda Wuta Da Ransa a Akwa Ibom

Advertisements


Hankulan mutane sun tashi a garin Ikot Afunga a karamar hukumar Essien Udim a jihar Akwa Ibom a jiya Litinin a yayin da yan daba suka sake cinnawa wani dan sanda mai mukamin sufeta wuta a gidansa.

An gano cewa yan daban sun afka gidan dan sandan mai suna Aniekan misalin karfe 2.30 na dare suka zagaye gidan suka cinna wuta a lokacin yana barci, Vanguard ta ruwaito.

Wannan shine karo na uku da yan daba ke kai wa yan sanda hari a gida da caji ofis a karamar hukumar. Idan za a iya tunawa a ranar 22 ga watan Fabrairun 2021, yan daba sun kai hari a Ikpe Annang Junction, sun kone dan sanda da ransa a cikin motar sintiri yayin da saura suka gudu.

Wani mazaunin unguwar da ya nemi a boye sunansa yace kisar ba zai rasa nasaba da rawar da dan sandan ya taka ba wurin tsare masu laifi da gurfanar da su a kotu.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Mr Odiko MacDon ya tabbatar da afkuwar inda ya ce abin bakin ciki ne kuma ana bincike.

“Kwamishinan yan sandan jihar, Mr Andrew Amiengheme ya nuna bakin cikinsa kan afkuwar lamarin ya kuma yi wa iyalan mamacin ta’aziya. Ya bada umurnin yan sanda su bazama bincike a garin. Ana cigaba da bincike a yanzu kuma ya bada tabbacin za a kamo wadanda ke da hannu a hukunta su.

 DAGA BZ NEWS 24/7

Advertisements

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like