Jinkai: Kalli Hotunan Kaga Yadda Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji

Advertisements


An gano gwamna jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a baya bayan nan ya tsaya tare da ayarin motocinsa ya taimakawa wasu mata da ‘yan mata da ke diban itace a gefen titi. A wasu hotuna da suka bazu a dandalin sada zumunta, an gano gwamnan kewaye da hadimansa suna taimakawa wasu mata.

Babu tabbas game da ranar da abin ya faru ko kuma wurin da ya faru amma hotunan sun dauki hankulan mutane da dama a dandalin sada zumunta.

Duba da cewa abin da gwamnan ya yi ba lamari bane da ya fiye faruwa, mutane da dama sun ta yaba wa gwamnan kan tausayi da sanin ya kamata da ya nuna, yayin da wasu kuma ke ganin siyasa ce kawai. Hotunan sun nuna hadiman gwamnan sun loda itacen a bayan mota mai kama da Hilux da nufin taimakawa matan daukar kayan itacen da suka samo daga daji.

Kalli Hotuna akasa:

 DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

Advertisements

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like