Rashin Bada sadaka yasanya Mabarata sunyi zanga zanga a Jihar Oyo

Advertisements


Mabarata sun fito zanga zangar rashin samun sadaka daga mutanen gari -Wannan ya faru ne a jihar Ibadan a ranar Alhamis 1 ga watan Afrilu

Ana jitar jitar cewa masu kudi na amfani da mabaratan wajen yin tsibbu Akalla mabarata 250 a jihar Ibadan, ranar Alhamis, suka fito zanga zangar rashin samun sadaka daga jama’ar gari bayan wani jita jitar cewa masu hannu da shuni na amfani da su wajen tsibbu saboda wata manufarsu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A bisa rahoton, mai magana da yawun mabaratan, Imam Abubakar Abdullahi yace, sarkin Hausawa dake Oja’aba, a jihar Ibadan yayi matukar tsanar mutanan shi.

A cewar Abdullahi: “Rahoton dake yawo na cewa wasu masu hannu da shuni suna amfani da mabarata da wasu nakasassu wurin yin kudi da wasu tsubbu ba gaskiya bane. “A sanadiyyar hakane yasa mutane suka nesanta kansu daga wadannan bayin Allah.

“Abinda muka sani shine yan kasuwa, masu talla da direbobi suna zuwa wurin mabaratan nan wadanda yawancinsu makafi ne da guragu suyi chanjin kudi. “Muna so mu wanke kanmu saboda mutane su daina azabtar da mu akan laifukan da bamu da masaniya akai.”

SOURCE: LEGIT.NG

 DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

Advertisements

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like