Yanzu yanzu: Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban ‘yan sandan Najeriya, duba sunansa da karin bayani gameda dashi anan>>

Advertisements


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, a matsayin sabon sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya. Ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda wa’adin mulkinsa ya kare.





Ministan harkokin ‘yan sandan Najeriya, maigari Dingyadi ne ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati.





A ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin mulkin shugaban ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu. Alkali zai karba ragamar mulkin ‘yan sandan Najeriya ne a take.

Advertisements





Karin bayani na nan tafe…





Source: Legit


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like