Advertisements
Abena Moet wacce ta yi aure kasa da makonni uku ta ba mutane da yawa mamaki a shafukan sada zumunta da cewar da tayi babu wani abu na musamman game da aure
A wani bidiyo mai ban dariya, ta ambaci cewa a cikin aure, kawai miji na aiken matar ne yadda ransa yake so
An gano ta a cikin bidiyo tana kallon kafadunta don tabbatar da cewa mijinta baya sauraron abunda take fadi Shahararriyar matashiyar nan ta kasar Ghana,
Abena Moet, ta haddasa cece kuce game da ra’ayinta a kan aure bayan shafe kusan makonni uku a gidan miji.
Advertisements
A cikin bidiyon barkwancin da ke yawo a shafukan sada zumunta, Abena Moet ta nuna cewa daga abin da ta gani, da zaran kin yi aure a matsayinki na mace, toh kawai mijinki zai ta aikenki ne yadda ransa ke so.
An gano ta a bidiyon tana kallon kafaɗarta don tabbatar da cewa sabon mijin nata ba ya jin abunda take fadi a bidiyon nat Abena Moet ta yi aure a wani kasaitaccen biki da ya bazu a yanar gizo a ranar 27 ga waran Maris, 2021.