Advertisements
Hukumar EFCC a yanzu haka tana yi wa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari tambayoyi kan wasu zarge-zargen cin hanci da rashawa
An tattaro cewa an rike tsohon gwamnan a ofishin hukumar na Sakkwato na tsawon awanni takwas har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton a ranar Talata, 20 ga watan Afrilu
Majiya ta ce an bayar da belin Yari amma bai iya cika sharuddan belin ba Jaridar Premium Times ta rahoto cewa yanzu haka tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, yana hannun hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).
A cewar rahoton, jami’an EFCC na yi wa Yari wasu tambayoyi kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.
Advertisements
An ce an tsare tsohon gwamnan a ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Sakkwato tsawon awanni takwas a daidai lokacin rubuta wannan rahoton.
majiya da aka nakalto a cikin rahoton ta ce: “Ya amsa gayyatar a ofishin Sakkwato da misalin karfe 11 na safiyar Talata. An basa beli, amma bai iya cika sharuddan belin ba.”