Da duminsa: Mahaifiyar sarkin Kano, Maryam Bayero, ta rasu,

Advertisements


Maryam Bayero, mahaifiyar sarkin Kano Aminu Bayero ta rasu Marigayiyar ta amsa kiran mahaliccinta a yau Asabar, 24 ga watan Afrilu a wani asibitin Alkahira, Masar,

Wata majiya na iyalan ta tabbatar da mutuwar tata Allah ya yi wa mahaifiyar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, Hajiya Maryam Bayero rasuwa.

Marigayiyar, wacce ta kuma kasance uwa ga sarkin Bichi, Nasiru Bayero, ita ce matar marigayi Sarki Ado Bayero mafi tsufa da ke raye.

Majiyoyi na iyalin sun tabbatar da mutuwar tata, inda suka ce ta mutu ne a safiyar ranar Asabar, 24 ga watan Afrilu a wani asibitin Alkahira, Masar, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Advertisements

A gefe guda, mun ji cewa Allah ya yi wa Buhari Abubakar III, yayan Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar rasuwa, Daily Trust ta ruwaito.

Kafin rasuwarsa, Buhari ne ke rike da mukamin hakimin Sokoto ta Arewa. Ya rasu ne a asibitin koyarwa ta Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Source: Legit


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like