Kalli Bidiyon Ango yana yiwa DJ da Amaryarsa Fada a ranar biki wanda ya janyo cece-kuce

Advertisements


Wani bidiyo wanda ya dade yana yawo a kafafen ra’ayi da sada zumunta ya jnayo cece-kuce – Bidiyon ya nuna wani Ango yana warwarewa DJ da Amaryarsa yayinda aka bukaci su yi rawa

Bayan gaisawa da wasu mata, Angon ya jawa DJ kunne kada ya kuskura ya ce yayi rawa Bikin aure a Najeriya taro ne dake cike da farin ciki da shewa,

amma a wani daurin aure, mutane sun yi mamakin yadda Ango ya tsawatawa mutumin da suka gayyata tsara taron. Hakazalika, ya tafi ya bar amaryarsa a tsaye saboda fushin da yayi a bainar jama’a.

Duk da yunkurin da DJ din yayi, Angon ya lashi takobin cewa ba zai yi rawa ba kuma Amaryarsa ba za tayi rawa ba. Ba tare da bata lokaci ba, yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan faifan bidiyo.

Yayinda wasu ke cewa Angon ya yi zafi da yawa, wasu sun ce bai kamata yayi haka a bainar jama’a ba. Wasu kuma sun ce Allah ya basu zaman lafiya, amma sai Amaryar ta yi hakuri.

Kalli bidiyon aqasa:

Advertisements

Omo, watch the shocking moment the where the Groom refused to dance and warned the MC to stop telling him to dance 😯😧 pic.twitter.com/Li9Y3Rsm4Q

— Osama🌚 (@osirmah) April 22, 2021
Umana Ak Umana yace: “Ka tsaya kan bakanka kuma kaka kayi rawan. Kawai ka kula da matarka kuma kayi addu’a Allah ya baku rayuwa mai tsawo.”

Stanley Chimezie Ibeke: “Wannan ra’ayinsa ne kuma ya kamata a girmama hakan. Na jinjinawa jajircewansa. Wannan namiji ne.”

It’z Hola Drizzy: Tun da ya san shi Ustazu ne me yasa aka gayyacu DJ.” Leo Kidze Kidze: “Kai Ustaz ne amma kana gaisawa da mata a jere. Wayo man” Anas Muhammad: “Wannan zabinsa ne, abinda yake so kenan kuma ba matsalanmu bane.”

Source: Legit.ng


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like