Kalli Hotunan motocin alfarman na miloniya Ahmed Musa masu darajar N200m sun gigita jama’a

Advertisements


A cikin kwanakin nan ne Ahmed Musa ya koma kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars – Kyaftin din kungiyar Super Eagles ya bugawa Najeriya wasanni 96

An ga Musa tsaye a gaban garejin motocinsa na alfarma da zasu kai darajar N200m Kyaftin djn Super Eagles, Alhmed Musa, yana daya daga cikin ‘yan wasan kwallon kafa a Afrika masu tarin dukiya duba da makuden kudaden da ya samu tun daga fara wasan kwallon kafarsa.

Kwanaki sun shude kuma ya zama labari, lokacin da Musa ke wasa kwallon a titunan Jos. A yanzu matashin mai shekaru 28 ya tara motocin alfarma a garejinsa kuma yana rayuwa mai cike da hutu.

Bayan kammala gina filin wasanni a jihohin Kano da Kaduna, ya bayyana cewa zai tamfatsa makaranta da zata yi gogayya da wasu makarantun na duniya a garin Jos.

Ahmed Musa ya wallafa hotonsa a shafinsa na kafar sada zumuntar a ranar Juma’a, 23 ga watan Afirilu, inda ya tsaya gaban katafaren ma’adanar motocinsa.

Advertisements

A garejin dake bayan Ahmed Musa a hoton, an ga manyan motocin alfarma guda biyu kirar Jeep wanda suka nuna tsabar ajin dan wasan kwallon kafan.

Wata mota kirar Range Rover fara da wata motar kalar bula kirar Toyota Jeep. Musa ya tsaya a gaban motocin inda yake murmushi tare da yi wa masoyansa fatan Juma’a ta gari.

A cikin kwanakin nan ne Ahmed Musa ya koma kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars bayan kasa komawa Turai da yayi kuma zai zama tare da Sai Masugida har zuwa karshen kaka.


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like