Yanzu yanzu: ‘Yan bindiga sun hari coci, sun kashe likita, sun sace mutane Kaduna

Advertisements


Har ila yau, ‘yan bindiga sun far wa masu bautar addinin kirista a cocin da ke kauyen Manini Tasha a karamar hukumar Chukun da ke jihar Kaduna, a safiyar Lahadi.

An kashe mutum guda, wanda aka bayyana a matsayin likita, yayin da maharan suka sace wasu masu bautar da dama. Wani ganau, wanda da kyar ya tsere daga abin da ya faru a Cocin na Haske Baptist da ke kauyen Manini,

Mista Yakubu Bala, ya shaida wa Leadership cewa ’yan bindigan da ke dauke da muggan makamai sun kutsa kai cikin cocin inda suka yi wa masu ibadan dirar mikiya da misalin karfe 9 na safe.

Ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun zo ne da yawansu, dauke da muggan makamai kuma suka fara yin harbi ba kakkautawa kan masu bautar, wadanda suka yi ta neman tsira a wurare daban-daban.

Advertisements

Karin bayani nan gaba kadan…

Latsa Nan: Shiga Group dinmu a whatsapp domin samun labaranmu akoda yaushe


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like