JAMB ta daga ranar yin jarabawar gwaji ta wannan shekarar Duba dalili

Advertisements


Hukumar JAMB ta dage ranar rubuta jarabawar gwaji ga daliban da suka yi rijista a wannan shekarar

Wannan sanarwan na kunshe ne a wata takarda da jami’in hulda da jama’a na hukumar ya fitar a ranar Lahadi,

An mayar da jarabawar zuwa ranar Alhamis, 20 ga watan Mayun 2021 a maimakon 20 ga watan Afirilu Hukumar JAMB ta daga jarabawar gwajinta da ta saka za a yi a ranar Asabar, 30 ga watan Afrilu zuwa ranar Alhamis, 20 ga watan Mayun 2021, Daily Trust ta ruwaito.

A wata takarda da Fabian Benjamin, shugaban fannin hulda da jama’a na hukumar, yace sauyin ranakun ya biyo baya ne sakamakon wasu ‘yan gyare-gyare da hukumar ke yi.

“Sauyin ba zai shafi ranar asalin jarabawar ba da aka saka daga 5 zuwa 19 ga watan Yunin 2021. Ana bukatar daliban da suka yi rijista tare da bukatar zaunawa jarabawar gwajin da su kiyaye sauyin ranakun da aka samu,” yace.

Yace ya zama dole a sanar da dukkan masu ruwa da tsaki cewa ana cigaba da rijistar UTME kuma za a rufe a ranar 15 ga watan Mayun 2021.

Advertisements

“Hukumar ta gano cewa, wasu masu son rubuta jarabawar na kokarin fara cike muhimman abubuwansu amma suna tura abinda bai dace ba ga 55019 ta layin wayarsu.

“Ana tura NIN ne tare da barin tazara a tsakanin sannan a rubuta lambar NIN din ga 55019. Misali NIN 00000000000.”

Yace duk wata hanyar da bata dace ba da aka bi ba zata sa a fara yi wa dalibi rijista ba. “Ya zama dole mai rubuta jarabawa su gane cewa sai layin wayan da aka hada da NIN ce za a iya amfani da ita wurin rijista,” yace.

Source: Legit


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like