Advertisements
Mujallar yaɗa labarai a matakin ƙaramar hukumar Dambatta wato FITILAR DAMBATTA ta sake shirya gasar tseren keke a karo na biyu (2) a Karamar Hukumar Dambatta da Makoda.
Da yake magana shugaban kwamitin tsare tsare na gudun tseren, Auwalu Nakarkata Dambatta ya ce, nan bada jimawa ba za’a sanar da lokacin da za’a fara sayar da form din shiga gasar kamar yanda aka yi a baya.
Auwalu ya ƙara da cewa; ana shirya wannan gasa ne domin sada zumunci tsakanin matasa da nishadantar da al’ umma da nunawa jama’a mahimmanci motsa jiki ga lafiyar ɗan Adam.
Auwalu ya ƙara da cewa; a wannan karon mun faɗaɗa wasan har zuwa Ƙaramar Hukumar Makoɗa dan kara dankon zumunci da karfafa alaƙa tsakanin matasan yankunan biyu.
Advertisements
A karshe akwai kyaututtuka masu yawa ga wanɗanda suka lashe wannan gasa daga gurbi na daya (1) har zuwa na Uku (3). Sannan akwai shaidar karramawa da za a ba kowane Ɗanwasa. Kwai kyaututtukan da muke sa rai za a samu daga hannun jama’a kamar yanda aka samu a waccan karon. A wannan karon idan an samu da yawa za duba yiwuwar bayar da kyauta har zuwa na biyar (5).
- ‘Da Zai Maka Ubansa A Kotu Bisa Kin Biyansa Kudin Kwangila Da Ya Aiwatar
- ‘Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa’, Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika
- ‘Yan Arewa Ga dama ta samu: Cikakken Bayanin yadda zaku zuba Hannun Jari a Kamfanin MTN NG kusamu Gajiyar hakan, Zasu siyar da kowacce hannun jari Daya Akan farashin N169.00
- ‘Yan Arewa masu kishi anfara Daukar Ma’aikata: Masu Kwalin Diploma Ko NCE Level ( 06 ), SSCE Level (03, 04) Ku Karanta Wannan Sakon Kafin Cike Aiki A Hukumar Kwastam ta Najeriya
- ‘Yan Arewa Mu Farka: Wadanda Basu Cike Abaya Ba, Su Garzaya Ansake bude Shafin NYIF Suje Su Cike Dan Allah Kuyi Share Zuwa Ga Sauran Mutane