An Cafke Matashin da Ya Sace Wayoyin Naira Miliyan 15 a Katsina

Advertisements


Yan sanda a jihar Katsina, a ranar Juma’a sun kama wani tsohon mai laifi da wayoyin salula na sata guda 273 da kudinsa ya nai Naira miliyan 15, Premium Times ta ruwaito.

Kakakin yan sandan, Gamba Isah, ya ce wanda ake zargin, Ibrahim Lawan, dan shekara 23, mazaunin Fegi Quaters a karamar hukumar Daura ya kutsa cikin mota ne ya sace wayoyin

Yan sandan sun ce a ranar 22 ga watan Afrilu aka sace wayoyin amma bayan an shigar musu da korafi, yan sandan suka yi nasarar kama wanda ake zargin

“Wanda ake zargin da ake kira ‘Abba Kala’ (Abba Swags) hatsabibin barawo ne, tsohon mai laifi, wanda ya saba da shiga gidan mutane yana sata da kuma satan babur,” in ji yan sandan.

“Dubunsa ta cika yayin da wanda ake zargin ya kutsa gidan wani Kamalu Ibrahim, dan shekaru 33, mazaunin Shagari Low Cost, Daura, ya balle motarsa, BMW 3 Series mai lamba JW 01 DRA ya sace wayoyin.

Advertisements

“An gano dukkan wayoyin 273 da ya sace a tare da shi a yayin da yan sanda ke bincike.

“Wanda ake zargin ya amsa laifinsa a hannun yan sanda. Za a gurfanar da shi da zarar an kammala bincike,” in ji kakakin yan sandan.

Source: Legit
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like