Advertisements
Wata fasto mace ta zage mambobin cocinta da tsinuwa bayan sun ki tara mata kudin shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta
Faston da ta bayyana wani bidiyon da ke yawo a kafar sada zumunta, an ji tana kiran mambobin cocinta da shaidanu saboda makon da suka nuna mata
An ji tana cewa ba amfanin kanta za ta yi da kudin ba, su za ta hadawa abincin da zasu ci saboda wasu daga cikinsu kamar aladu suke
Wata fasto ta yi tofin Allah tsine ga mambobin cocinta sakamakon kin tara mata kudin shagalin murnar bikin zagayowar ranar haihuwarta da suka yi.
A wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani, an ji faston tana kiran mambobin cocinta da shaidanu saboda kin yi mata wannan kara da suka yi.
“Ko a ranar zagayowar haihuwata, wasu daga cikinku sun ki bada kudi. Ubangiji zai ladabtar da ku saboda baku da tausayi, sai dai kuma idan baku da kudin.”
Advertisements
“Ba wai kamar kudin nawa bane, na abincin da zaku zo ku ci ne. Wasu daga cikinku mugun ci garesu kamar aladu kuma sai kun kwasa wani abincin kun tafi da shi gida,” faston tace.
Ga bidiyon nan mai karatu ya kalla a kasa:
Pastor’s wife cursing Church members because they did not contribute money for her birthday.pic.twitter.com/8SWp5NHfmY
— Laila Ijeoma | Lailasnews.com (@LailaIjeoma) May 2, 2021
Source:legit
- APPLY NOW: GREAT Scholarships offer students from 14 countries
- Melbourne International Undergraduate Scholarship 2023 | Study in Australia
- APPLY NOW: Khalifa University Scholarships in UAE 2023 | Fully Funded
- APPLY: Commonwealth Professional Fellowships 2023-2024 in United Kingdom
- APPLY: Leeds University Business School Scholarship 2023/24 | Fully Funded | Study in UK