Yanzu yanzu: NECO ta saki sakamakon jarrabawar 2020

Advertisements


Hukumar jarrabawar kammala sakandare a Najeriya ta NECO ta saki sakamakon jarrabawar na shekarar 2020.

Hukumar ta National Examination Council ta sanar da hakan ne a birnin Minna na Jihar Neja a yau Alhamis.

Rajistira kuma shugaban hukumar, Godswill Obioma, ya ce ɗalibai 41,459 ne suka yi rajistar rubuta jarrabawar, sai dai 39,503 daga cikinsu ne suka rubuta ta.

Ya ce an samu waɗanda suka aikata ba daidai ba guda 6,465 a 2020, ba kamar a 2019 ba inda aka samu 17,004.

Advertisements

Ya ƙara da cewa ɗalibai 26,277 sun samu kiredit biyar zuwa sama ciki har da Ingilishi da lissafi, yayin da 34,014 suka samu kiredit biyar ɗin ba tare da maudu’an guda biyu ba.

Shugaban wanda ya jaddada matsayar hukumar wajen ƙin amincewa da ayyukan rashin gaksiya, ya ce sun bi dukkan matakai da ƙa’idoji kafin sanar da sakamakon.

Source: Bbc Hausa
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like