Da Duminsa: Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Ƴan Sanda da Ƴan Acaɓa a Legas

Advertisements


An shiga zaman ɗar-ɗar a Ogba, jihar Legas kan zargin harbe wani ɗan acaɓa da wani ɗan sanda ya yi. Wata majiya ta shaidawa The Punch cewa rikicin ya fara ne tun juya a lokacin da ɗan sandan ya ƙi biyan ɗan acaɓan kudin ɗaukansa da ya yi.

Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa an kashe mutum biyu a daren jiya Alhamis. “Faɗa ne tsakanin ƴan sanda da ƴan acaɓa.

Ɗan acaɓa ya ɗauki ɗan sanda zuwa wani wuri a jiya, sai ya tambayi kuɗin aikinsa daga hannun ɗan sandan bayan ya sauke shi. Ɗan sandan ya ƙi biyan shi kuɗin sannan ya harbe shi.

Advertisements

“An ji ƙarar harbe-harbe a yau da safe. Mintuna ƙalilan da suka shuɗe. Dukkan ƴan acaɓa sun sauka daga baburansu suna shirin yin zanga-zanga,” a cewar majiyar. Ku saurari ƙarin bayani …

Source: Legit
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like