Advertisements
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya gudanar da sallar Idi tare da dimbin mabiyansa ranar Laraba.
Malamin ya gudanar da sallar Idi ne a gidansa da ke birnin Bauchi a arewa maso gabashin kasar.
Daya daga cikin ‘ya’yan malamin, Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi, shi ne ya ja sallar ta Idi yayin da malamin yake cikin mamu.
Bayan idar da sallar, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce sun gudanar da sallarsu ta Idi ne saboda an tabbatar musu da ganin watan Shawwal ranar Talata.
A cewarsa, “Dangane da wadannan labarai na cewa wata ya tabbata, abin da aka ce adilai guda biyu idan sun gani ya isar mana jama’a, ko kuma jama’a masu yawa [idan sun ga watan].”
Ya kara da cewa an ga wata a wurare irin su Gombe da Gadau da kuma Kebbi.
Advertisements
Shiekh Dahiru Bauchi ya ce ba su da ikon karyata mutanen da suka tabbatar da ganin wata “saboda suna da yawa. Shi ya sa yanzu muka zo muka gudanar da Sallah Idi domin watan Ramadana ya kare, watan Shawwal ya shigo.”
Galibin Musulman Najeriya za su gudanar da sallar Idi ce ranar Alhamis bayan Kwamitin da ke bai wa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addini tare da hadin gwiwar Kwamitin Duban Wata a Najeriya sun ce ba su samu rahoton ganin jaririn watan Shawwal a Najeriya ba ranar Talata 11 ga watan Mayun 2021 wanda ya yi dai-dai da 29 ga watan Ramadan 1442 AH.
Hakan ne ya sa Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana Alhamis 13 ga watan Mayu 2021 a matsayin ranar Sallah kuma 1 ga watan Shawwal.
Source: Bbc Hausa
- APPLY NOW: GREAT Scholarships offer students from 14 countries
- Melbourne International Undergraduate Scholarship 2023 | Study in Australia
- APPLY NOW: Khalifa University Scholarships in UAE 2023 | Fully Funded
- APPLY: Commonwealth Professional Fellowships 2023-2024 in United Kingdom
- APPLY: Leeds University Business School Scholarship 2023/24 | Fully Funded | Study in UK