Yanzu yanzu: (JAMB) Ta Saki sabuwar sanarwa gameda zana jarrabawar (JAMB) ta shekarar 2021,

Advertisements


Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB) ta ce akwai yuwuwar ta sauya lokacin rubuta UTME ta 2021

Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya sanar da hakan a yayin ganawar da yayi da masu ruwa da tsaki a ranar Juma’a

Farfesan yace wannan cigaban zai zo ne sakamakon yadda dalibai suke shan wahala yayin yin rijistar jarabawar,

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB) ta fara magana a kan yuwuwar sauya lokacin rubuta jarabawar na shekarar 2021.

Dama za a rubuta jarabawar ne daga ranar 6 ga watan Yunin 2021 zuwa ranar 19 ga watan Yunin 2021.

Hukumar shirya jarabawar amma ta tabbatar da cewa za a rubuta jarabawar gwajinta a ranar 20 ga watan Mayun 2021 bayan sauya ranar da tayi.

Advertisements

Hukumar ta ce hukuncin dage jarbawar ko rubutata za a yanke shi ne a ranar Juma’a bayan kammala taro tsakanin hukumar da masu ruwa da tsaki.

Rijistra na hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya sanar da hakan a ranar Juma’a yayin taron da yayi da masu ruwa da tsaki a kan jarabawar ta yanar gizo.

Farfesa Oloyede ya dora laifin wannan cigaban a kan wahalar da dalibai masu rijistar jarabawar ke samu, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya ce a kalla dalibai 600,000 ne suka bayyana ra’ayinsu na rubuta jarabwar UTME ta 2021 amma har yanzu sun kasa yin rijista.

Source: Legit
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like