Yanzu-yanzu: Isra’ila ta rusa ofishin gidan jaridar Aljazeera dake Gaza, Falasdin

Advertisements


Kasar Isra’ila ta kai hari gidan benen da ofishin gidan jaridar AlJazeera, AP da wasu kamfanonin jaridar ke ciki a birnin Gaza, kasar Falasdin.

A bidiyon da Alarabiya ta dauka, an ga yadda makami mai linzami da Isra’ila ta harba ya rusa ginin har kasa.

Mai ginin benen, Jawwad Mahdi, ya bayyana cewa hukumar Sojin Isra’ila ta kirashi cewa za’a kaiwa gidansa hari.

Ya bayyana cewa an fada masa ya sanar da wadanda ke cikin ginin su tattara inasu-inasu su bari cikin awa guda.

Advertisements

Kalli bidiyon:

Watch: An Israeli airstrike flattens a high-rise building housing the AP and other media offices in #Gaza City. #Palestinehttps://t.co/tGXr5Kf0AR pic.twitter.com/qwqMSVi5iJ


— Al Arabiya English (@AlArabiya_Eng) May 15, 2021

Source: Legit
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like