Yanzu yanzu: Hedkwatar tsaron Najeriya ta sanar da dalilin hatsarin Babban hafsan sojin kasa -COAS Attahiru

Advertisements


Hedkwatar tsaron Najeriya ta sanar da cewa yanayin gari mara kyau ne yayi sanadin hatsarin jirgin saman COAS Attahiru

Kamar yadda hedkwatan tsaron ta sanar, tace jirgin ya sauka a filin sauka da tashin jiragen na Kaduna sannan ya tarwatse Duk da Janar Lucky Irabor ya bukaci a cigaba da bincike a kan lamarin,

ya bukaci a basu goyon baya tare da fahimta yayin binciken Hedkwatar tsaro ta kasa ta bayyana dalilin da ya kawo tarwatsewar jirgin sama wanda yayi sanadiyyar mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya,

Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10 a ranar Juma’a, 21 ga watan Mayun 2021.

Kamar yadda Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun hedkwatar tsaro ya sanar, duk da ana cigaba da binciken sanadin lamarin,

hatsarin ya auku ne bayan jirgin ya sauka a filin sauka da tashin jiragen saman na Kaduna.

Duk da da dai, Nwacukwu ta shafin hedkwatar tsaron na Twitter, ya bayyana cewa Janar Lucky Irabor, shugaban ma’aikatan tsaro ya bada umarnin binciken lamarin da ya kawo mummunan hatsarin.

Advertisements

Mai magana da yawun hedkwatar tsaron yace: “Mummunan lamarin ya faru ne bayan saukar jirgin a filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna saboda yanayin gari mara kyau.

“Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor ya bukaci bincike domin gano dalilin da ya kawo hatsarin.

“A yayin da muke fatan rahama ga zakakuran dakarun sojin da shugaban sojin kasan, AFN na bukatar goyon bayanku da kuma fahimta daga dukkan ‘yan Najeriya a kan wannan lamarin da ya faru.”

#PressRelease #DHQUpdate


ARMED FORCES OF NIGERIA LOSES CHIEF OF ARMY STAFF AND TEN OTHERS IN AIR MISHAPhttps://t.co/y9nQ8nuQwP


— DEFENCE HQ NIGERIA (@DefenceInfoNG) May 21, 2021Source: Legit


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like