Mansurah Isah ta sanar da rabuwar aurensu da Jarumi Sani Danja duba abinda tace,

Advertisements

Tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta tabbatar da rabuwa aurensu da jarumi Sani Danja

Ta sanar da hakan ne a wata wallafa da tayi a shafinta na Instagram amma ta goge bayan minti 4

Jarumar tace rabuwarsu ce mafi a’ala duk da kuwa albarkar da suka samu na ‘ya’ya hudu, mace daya, maza uku A cikin kwanakin da suka gabata ne ake ta rade-radin rabuwar aure tsakanin jarumi Sani Danja da matarsa, tsohuwar jaruma Mansurah Isah.

Hakan ya biyo bayan wata wallafa da tsohuwar jarumar tayi a shafinta na Instagram amma ta goge bayan minti hudu kacal.

Sai dai duk da gogewar da tayi, akwai wadanda suka ga rubutun amma da kyar mujallar fim ta samo wanda ya dauka hoton rubutun saboda rashin dadewar da yayi a shafinta na Instagram din.

Kamar yadda tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta wallafa, tace rabuwar aurenta da Jarumi Sani Danja shine mafi a’ala a garesu baki daya.

Idan zamu tuna, jaruman sun yi aure ne a shekarar 2007, auren da koyaushe ake kwatance da shi idan aka ce jaruuman Kannywood basu zaman aure kuma aurensu baya karko.

Advertisements

Allah ya albarkaci auren da ‘ya’ya hudu, mace daya, Khadijatul Iman da kuma yara maza hudu masu suna: Khalifa Sani, Yakubu da Yusuf.

An gano cewa ba wannan ne karon farko da Jarumi Sani Danja ya fara sakin matarsa ba, ya taba sakinta a lokacin da suke zama a Abuja, zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Jonathan amma sai aka sasantasu.

Kamar yadda Mansurah Isah ta wallafa a shafinta na Instagram: “Muna bada hakuri a kan kunyar da muka baiwa masoyanmu, ‘yan uwa da abokan arziki.

“Ni da Sani Danja bamu tare. Bamu son batawa kowa amma wannan rayuwarmu ce kuma hukuncinmu ne. “Muna son kowa ya mutunta haka saboda mun san ma’anar hakan. Mun damu da juna kuma a koyaushe muna taimakon juna.

“Amma muna tunanin hakan ne yafi dacewa. Akwai bukatar ya cigaba a rayuwarsa nima haka. Mun gode da fahimtarku.”

Source: Legit

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like