Bidiyon dan Najeriya mazaunin Turai: Zan dawo da tankar yaki na shiga Sambisa,

Advertisements


Wani dan Najeriya da ke kasar waje ya sha alwashin dawowa gida dauke da tankar yaki don kare kasar daga ‘yan ta’adda

Mutumin ya bayyana cewa, nan da makwanni hudu zai shiga da tankar yakin Najeriya don fara aikinsa na gyaran kasa

A cewarsa, zai tuka tankara yakin zuwa dajin Sambisa da kansa da zaran ya iso Najeriya nan ba da jimawa ba,

Wani dan Najeriya da ke zaune a kasar waje ya yi ikirarin cewa wani mutumin kirki ya bayar da gudummawar tankar yaki don yaki da rashin tsaro a kasar.

A wani bidiyo da @lindaikejiblogofficial ta wallafa a shafin Instagram, mutumin da ba a san ko wanene ba ya ce zai kawo tankokin yakin ne zuwa Najeriya inda zai yi amfani dasu wajen yakar mayakan Boko Haram, ‘yan bindiga, IPOB da ESN.

A cewarsa, tankar yakin din zata iso Najeriya nan da mako hudu. Ya ce zai tantance ta a tashar jirgin ruwa ta Tin Can a yankin Apapa da ke Legas.

A kalamansa: “Zai zama wuta ga wuta. Zan gama ku duka. Gaskiya na fusata kwarai da gaske.”

Advertisements

‘Yan Najeriya a shafin Instagram sun kasa daina dariya bisa lura cewa mutumin kawai wasa yake kuma bai kamata a saurareshi ba.

@legasha ya ce: “Lmao. Zai kashe ni da dariya.”

@ motayo41 yayi tsokaci: “Ba na son yin magana amma mutumin abin dariya ne.”

@ kic_ky4 ya rubuta: “Na yarda da kai yallabai, za ka iya yin haka tunda Sojojin ba sa son yin aikinsu.”

@ stalingrad326 ya ce: “Ahhhh mutanen kauye sun same shi, iyalansa don Allah ku taimaka masa.”

Source: Legit
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like