Yanzu yanzu: Wani Mutum Ya Shararawa Shugaban Faransa Emmanuel Macron Mari

Advertisements


Wani mutum da a yanzu ba a tantance ko wanene ba ya gaura wa Shugaban Kasar Faransa mari,

Lamarin ya faru ne a ranar Talata a yayin da Shugaba Emmanuel Macron ya ziyarci wani gari a kudu maso gabashin kasar

Bayan afkuwar lamarin Farai ministan Faransa Jean Castex da wasu yan siyasa a kasar sunyi tir da lamarin da suka ce yi wa siyasa karen tsaye ne Wani mutum ya mari Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa,

a ranar Talata yayin da tafi ganawa da mutanen gari a yankin kudancin kasar kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna, France 24 ta ruwaito.

Masu tsaron Macron sunyi gaggawa sun zakulo mutumin daga cikin dandazon mutane suka matsar da shi gefe. An kama wasu mutane biyu da hannu kan lamarin kamar yadda RMC radio ta ruwaito.

Reuters ta ruwaito cewa Farai Ministan Faransa Jean Castex ya ce lamarin karan tsaye na ga demokradiyya.

Lamarin ya faru ne a yayin da macron ya ziyarci yankin Drome da ke kudu maso gabashin Faransa inda ya ke ganawa da masu aikin sayar da abinci da dalibai domin tattaunawa da su kan yadda rayuwarsu ke tafiya bayan annobar korona.

Advertisements

A cikin faifan bidiyon da ya yawo a dandalin sada zumunta, an hangi Macron sanye da farar riga yana tafiya domin tarar da wasu dandazon mutane da ke jiran su gana da shi.

KARIN LABARAI:Shugaban na Faransa ya mika hannunsa ya gaisa da wani mutum mai sanye da t shirt launin kore sanye da gilashi da takunkumin fuska.

A yayin da aka mari shugaban Macron, an ji wasu suna ihu suna cewa “Allah wadaran akidar Macron”. Nan take masu tsaron Macron biyu suka damke mutumin yayin da wani guda ya matsa da shi gefe.

Sai dai Macron ya dauki wasu yan dakikai yana tsaye a wurin yana magana da wani. A halin yanzu ba a tabbatar da sunan mutumin ba da manufarsa.

SOURCE: LEGIT


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like