Anyi Rikici a Wurin Taron Jam’iyyar APC a Kano Duba Dalili

Advertisements

Rikici ya barke a wurin babban taron jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Kano, 

Rahotanni sun ce wasu daga cikin yan jam’iyyar ne suka fara dambe a yayin da ake gudanar da taron Barƙewar rikicin ya saka mutane sun fara tserewa amma daga bisani an magance rikicin an cigaba da taron, 

An samu barƙewar rikici a wurin taron gangami na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a Kano a ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito. 

Taron da ake yi a yankin Sabon Gari na jihar Kano, an shirya shi ne domin tarbar tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar Green Party of Nigeria, GPN, A.A. Zaura da wasu mutane da suka sauya sheka zuwa APC. 

A yayin da kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Rt Hon Hamisu Chidari ke yin jawabinsa, wasu mambobin jam’iyyar suka fara bawa hammata iska.

Advertisements

Daily Trust ta ruwaito cewa fadar da ta kaure tsakanin su ta kusa tarwatsa taron a yayin da mutane suka fara dare wa don gudun kada a raunata su. Sai dai bayan ɗan wani lokaci an dakatar da faɗan kuma abubuwa sun koma yadda suke. 

Kawo yanzu dai ba a tabbatar da abin da ya yi sanadin rikicin ba. Daga bisani an cigaba da taron. Rahotanni sun ce cikin wadanda suka hallarci taron domin komawa jam’iyyar na APC har da yan Kwankwasiyya wato magoya bayan tsoho gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso. 

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje yana daga cikin manyan baki da suka hallarci taron na tarbar sabbin mambobin na jam’iyyar APC. 

Source: Legit

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like