Mutumin da kifi ya hadiye kuma ya amayo shi, ya bada labari dalla-dalla duba abinda yace

Advertisements

Michael Packard mai shekaru 56 yace yana da sa’a tunda ya rayu bayan harin da kifi ya kai masa yayin da yake kan aikinsa a Massachusetts 

A yayin bayyana abinda ya fuskanta bayan kifin ya hadiye shi, yace tsabar bakikkirin komai ya koma masa yayin da yake cikin kifin 

Packard ya bayyana cewa ya kwashe dakika 30 zuwa 40 a cikin kifin kafin sa’a ta sa ya amayo shi waje Wani gagarumin gwanin nutso a kasar Amurka ya sha da kyar bayan da kifi ya hadiye shi kuma cike da sa’a ya amayo shi. 

Mutumin mai suna Michael Packard mai shekaru 56 yace yana da tsananin sa’a tunda ya rayu bayan farmakin da kifin ya kai masa yayin da yake aikinsa na kullum a Massachusetts. 

Daily Mail ta ruwaito cewa mutumin ya bada labarin yadda komai ya koma masa bakikkirin yayin da yake cikin kifin. 

Da farko yace zatonsa shark ne ya kai masa farmaki amma a lokacin da bai ji hakoransa ba, sai ya gane cewa ba shark bane. 

Advertisements

“Na gano cewa bakin kifi Whale nake ciki kuma yana kokarin hadiye ni. Daga nan na fara tunani, shikenan na mutu,” ya bada labari. 

The Insider ta ruwaito cewa mutumin ya tabbatar da cewa ya kwashe dakika 30 zuwa 40 a cikin kifin amma cike da sa’a aka samu ya amayo shi. 

“Kawai na ji an watso ni a iska kuma na fada ruwa. Dagan nan na gane na fito. Ga ni nan ina bada labarai,” Packard yace.

Wani mutum dake tare da mutumin mai shekaru 56 shi ya taimaka masa wurin fitar dashi daga ruwan. Duk da bai ji ciwo ba, ya dai samu guggurjewa a jikinsa. 

Source: Legit

DAGA: BZ NEWS 24/7

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like