Da dumi-dumi: An nada Alkalan Shari’a 34 a jihar Kano bayan gwaji

Advertisements

Babban Alkalin Jihar Kano, Mai Shari’a Nura Sagir, ya amince da nadin karin alkalai 34 a kotunan Musulunci da ke Jihar 

An amince da nadin alkalan ne bayan sun ci jarabawar da Hukumar Kula Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC) ta gudanar Za a rantsar da wadanda aka nada a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, a babbar kotun jihar 

Da amincewar Mai Shari’a Nura Sagir, babban alkalin Kano, an kara wasu alkalai 34 na kotun shari’ar Musulunci a jihar a ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni. 

Kakakin ma’aikatar shari’ar jihar, Baba Jibo-Ibrahim ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, jaridar Punch ta ruwaito. 

Advertisements

Jibo-Ibrahim a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa Babban Alkalin ya amince da nadin alkalan ne bayan sun ci jarabawar da Hukumar Kula Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC) ta gudanar, jaridar Aminiya ta ruwaito. 

Kakakin ya kara da cewa za a rantsar da wadanda aka nada a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, a babbar kotun jihar. 

Ya ce: “Ana bukatar sabbin Alkalan Kotunan Shari’ar Musuluncin da za a rantsar ranar Juma’a 25 ga watan Yuni 2021 da su hallara a Babbar Kotu da misalin karfe 10.00 na safe.” 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like