Wata makaranta a Kano ta amince iyaye su riƙa biyan kuɗin makaranta da ‘cryptocurrency’

Advertisements

Wata makaranta mai zaman kanta a jihar Kano, New Oxford Science Academy, ta fara karbar kudin makaranta da cryptocurrency 

Sabi’u Musa Haruna, shugaban makarantar ya tabbatarwa manema labarai hakan a ranar Alhamis yana mai cewa sun tuntubi iyaye kafin daukan matakin 

Musa Haruna ya bada misalin makarantun kasashen waje da suka karbar kudin crypto din da ya ce zamani ne ya zo dashi kuma ya yi imanin nan gaba kowa zai rungumi abin 

Wata makaranta mai zaman kanta a jihar Kano mai suna New Oxford Science Academy, Chiranci, ta ce tana karbar kudin crypto a matsayin kudin makaranta.

Shugaban makarantar, Sabi’u Musa Haruna, ne ya shaidawa manema labarai hakan a ranar Alhamis kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, 

Advertisements

A cewarsa, an amince da hakan ne bayan mahukunta a makarantar sun tattauna da iyayen dalibai. 

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Haruna ya kara da cewa an dauki matakin ne da nufin saukaka wa iyaye biyan kudin makaranta. Ya ce: 

“Mun amince za su rika karbar kudin crypto wurin biyan kudin makaranta saboda duniya ta fara karkata zuwa wannan tsarin. “Mun yi imanin cewa wata rana duniya za ta fi amincewa da kudin crypto fiye da kudin takarda.” 

Mr Haruna ya kara da cewa kasashe kamar El-Salvador da Tanzania tuni sun fara karbar kudin crypto a makarantunsu. 

Don haka, ya bukaci gwamnatin tarayyar Nigeria ta yi gaggawar rungumar tsarin ta kuma saka dokoki domin yin amfani da shi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like