Yanzu-Yanzu: Gwamnan Zamfara, Matawalle, Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar APC

Advertisements

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da sauya sheƙar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, daga PDP zuwa APC, 

Mai taimakawa shugaban ƙasa ta ɓangaren yaɗa labarai, Bashir Ahmad, shine ya bayyana haka a wani rubutu da ya fitar 

Sai dai a halin yanzu, gwamnatin Zamfara ba tace komai dangane da sauya shekar gwamnan ba, 

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da sauya sheƙar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, daga jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyya mai mulki ta APC. 

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da mai taikawa shugaban ƙasa Buhari ta ɓangaren yaɗa labarai, Bashir Ahmad, yayi a shafinsa na dandalin sada zumunta wato Facebook.

Advertisements

 Bashir Ahmad, ya rubuta a shafinsa cewa: “Zamfara ta dawo gida, lale marhabun gwamna Matawalle.” 

Sai dai a halin yanzu, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, bai tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa APC ba. 

A watan Afrilun da ya gabata ne gwamnonin PDP shida suka ziyarci gwamnan domin jawo hankalinsa kar ya koma APC. 

Gwamnonin sun haɗa da, gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, Nyesom Wike na jihar Rivers, Bala Muhammed na jihar Bauchi, Darius Ishaku na jihar Taraba, Umar Fintiri na jihar Adamawa da kuma Aminu Tambuwal na jihar Sokoto. 

Source: Legit

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like