Na Dauki Siyasa A Matsayin Addini — Shekarau

Advertisements

Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ba zai taba daina siyasa ba face mutuwa ce ta cimmasa domin kuwa ya dauke ta a matsayin addini.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, ya yi wannan furuci ne yayin ganawa da manema labarai bayan kaddamar da Majalisar Shura a gidansa da ke Unguwar Mundubawa a birnin Dabo.

Shekarau wanda ya yi gwamnan Kano tsawon wa’adi biyu kuma ya zama Ministan Ilimi a gwamnatin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya ce “bani da lokacin da zanyi ritaya daga siyasa har sai na mutu.

Shekarau wanda ke wakiltar Kano ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawa, ya ce, “dalilin da ya sa nake maimaita wannan batu shi ne, babu wani lokaci da zanyi ritaya daga siyasa.

“Fiye da tsawon shekara 20 ina fadin haka, siyasa ita ce addini na, kuma addini na shi ne siyasa.

“Saboda haka babu wani lokaci da zan bar wannan addini saboda duka su biyu suna aiki kafada-da-kafada da juna ne.

“Addini shi ne bauta wa Allah kuma mafi kololuwar bautar Allah ita ce hidimta wa al’umma wadanda Allah ne ya haliccesu.

“A mahanga ta addinin Islama, duk wanda ka taimaka wa, kana bin umarnin Allah ne.

“Idan na yi wa wani addu’a, ko na kyautata masa, hakan wani nau’ii ne na bautar Allah.

“Saboda haka ita siyasa babu abin da ta kunsa face yi wa al’umma hidima, kuma ba sai lallai mutum yana rike da wani mukami ba.

Advertisements

“Ko shekara 90 na kai ta yadda tsufa ba zai bari na tsaya takara ba ko kuma fita yawon yakin neman zabe, zan iya bayar da shawara ga jama’a ina kwance a bisa gado.

“Saboda haka ita siyasa wata hanya ce ta yi wa mutane hidima, wanda kuma hakan ita ce fahimta kuma akidar da na rika.

“Dalilin haka ya sa nake tausayin duk wanda yake tunanin ritaya daga siyasa, kila sai dai bai fahimci ko mece ce siyasa ba.

“Kasancewar galibi suna iyakance ta ne kadai da samun wani mukami, wadanda suka fahimci cewa idan ba wannan ba to mutum ba siyasa yake ba.

“To a gaskiya masu irin wannan tunani basu fahimci hakikanin abin da ake nufi da siyasa ba.

“Abin da na fahimta da siyasa shi ne samun damar yin mu’alama da jama’a da kuma hidimta musu ta kowacce hanya.

“Kuma in dai wannan ne babu lokacin da zan daina face ajali ne ya yi kira na.

“Ina fadin haka ne saboda na fahimtar da masu adawa da ni da ke yada jita-jitar ko kuma masu neman su debe wa magoya bayana tsammanin cewa Sardaunan Kano ya kusa ritaya.

“Wasu ma suna cewa ba zan sake tsaya wa takara ba, sai dai wannan ba maganar da ke gabanmu ba kenan don har yanzu ina da sauran shekara biyu kafin na kammala wa’adi na kuma wannan wata dama ce a gare ni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like