A Kano: Ɗalibi ya cinnawa kansa wuta saboda bai samu kuɗin biyan jarrabawar NECO

Advertisements

Wani ɗalibi mai shekaru 20, Ɗanladi Shuaibu ya cinnawa kansa wuta a Kano don ya gaza samun kuɗin NECO Rahotanni sun ce Shuaibu ya rubuta jarrabawar ta NECO sau uku a baya amma bai yi nasara ba 

Ya shiga matuƙar damuwa bayan ya gaza samun kuɗin biyan jarrabawar a bana hakan yasa ya cinnawa kansa wuta a ɗakinsa

Ɗanladi Shuaibu, wani ɗalibi mai shekaru 20 a jihar Kano, ya cinnawa kansa wuta don bai samu kudin biyan jarrabawar kammala sakandare ta SSCE ba, 

The Cable ta ruwaito. An ruwaito cewa Shuaibu mazaunin garin Garo a ƙaramar hukumar Kabo na jihar ya rubuta jarrabawar ta NECO sau uku amma bai yi nasara ba. 

NECO ta bayyana cewa za ta rufe yin rajistan jarrabawar 2021 a ranar 25 ga watan Yuni – kuɗin jarrabawar N9,850. Sau uku marigayi Shuaibu na rubuta NECO amma bai yi nasara ba

Advertisements

Iliya Ahmad, mazaunin garin, ya shaidawa The Cable cewa marigayi Shuaibu ya cinnawa kansa wuta bayan da farko ya yi barazanar zai kashe kansa idan bai samu kudin yin rajistan jarrabawar ba. 

A cewar Ahmad, lamarin ya faru ne a ranar Talata na makon da ta gabata a Garo. Marigayi Shuaibu ya yi ƙoƙarin neman kudin jarrabawar amma ya shiga damuwa bayan ya gaza samun kuɗin. 

Rahotanni sun ce a ɗakinsa ya cinnawa kansa wuta amma ihunsa ya janyo makwabta suka garzaya da shi asibitin Garo don masa magani. Amma, daga bisani ya ce garinku. 

A cewar wani mazaunin garin, marigayin na koyon kanikanci a wani gareji a Garo. Kakakin ƴan sandan Kano Abdullahi Kiyawa ya ƙi cewa komai game da lamarin a lokacin da aka tuntube shi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like