Kai tsaye: Yadda mukabala ke gudana tsakanin Malaman Kano da Sheikh AbdulJabbar Kabara

Advertisements

Bayan kai komo da aka yi kan batun mukabalar Sheikh Abduljabbar, an sanya ranar da za a caccaka tsinke tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano Zasu zauna zaman mukabala a yau ranar Asabar, 10 ga watan Yuli. 

An fara mukabalar A cewar BBC Hausa, Sheikh Rabiu Rijiyar Lemo ne ya fara yi wa Abduljabbar tambaya kan auren Annabi SAW da Safiyatu da kuma batun yin fyade da tsirara. 

Malam Rabiu ya nemi Abduljabbar ya kawo masa hadisin a Sahihul Bukhari. AbdulJabbar ya bada amsa da cewa Anas ɗan malik shi ya kore hadisin “kore wa ma’aiki kalaman da ake masa batanci yake yi” 

Sai dai an Malam Rabi’u Rijayar lemo ya ce bai bayar da amsar dai dai ba, inda ya ce hadisin ya bambanta da abin da ya faɗa. 

Advertisements

Farfesa Salisu Shehu ne Alkalin mukabalan Shugaban jami’ar Al-Istiqama Sumaila, Farfesa Salisu Shehu, ne Alkalin mukabala 

Malamai sun shirya tsaf don fara mukabala Sheikh AbdulJabbar Kabara da tawagarsa sun dira wurin mukabalar. Hakazalika sauran Malamai sun Isa wurin da aka shirya mukabala a yau Asabar. 

Daga ciki akwai Ustaz Kabir Bashir Abdulhamid, Dr Muhammad Rabiu Rijiyan Lemo, Malam Lawal Triumph, dss. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like