Advertisements
Shugaban Darikar Tijjaniya a Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce Aljanu miliyan uku su ka karbi Darikar Tijjaniya
Babban Malamin ya ce daga cikin wadannan Aljanu, akwai mukaddamai miliyan dari biyu Akwai yiwuwar a rika amfani da Aljanun domin maganin masu garkuwa da mutane.
Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi wata magana wanda ta ba dinbin mabiyansa da sauran al’umma mamaki.
Shehin malamin ya bayyana cewa akwai wasu kebantattun mutane da su ke iya sadu wa da aljanu. Ya ce ya na daga cikin masu mu’amala da su.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce wasu suna ganinsu, har su yi magana da su, kamar yadda shaidanun mutane su ke hulda da shaidanun Aljanu.
A cewar Sheikh Dahiru Usman Bauchi akwai Aljanu muminai, daga cikin su har mabiya Darikar Tijjaniya wanda yanzu adadinsu ya zarce biliyan uku.