Nayi nadamar duk karuwancin da nayi a baya, yanzu ko kudin magani bani da shi – Muneera

Advertisements

Muneerat Abdussalam, fitacciyar mai maganin mata da maza wacce take tallata hajarta a kafafen sada zumuntar zamani ta bayyana yadda bariki tayi mata atishawar tsaki.
A cewarta, ta yi nadamar karuwanci, shashanci da lalatar da ta dinga yi da mazan banza kuma yanzu komai ya kare mata don ko kudin maganin da za ta sha sakamakon ciwon da ke damunta ba ta da shi.
Muneerat Abdussalam ta yi bayani dalla-dalla akan bakin dukan da taci a hannun saurayinta wanda tace sun koma zaman dadiro tun bayan ya yi mata alkawarin zai aure ta.
A cewarta, ya lamushe mata kayan sana’a na makudan kudade wadanda ta aike shi ya sanya mata su a mota, daga baya kuma ya biyota har daki ya tumurmusheta yadda yaga dama.
Ga abinda ya bayyana a shafinta na Facebook “Oh ni Muneerat Abdulsalam  haka ratuwata ta koma? Ko kudin sayan paracetamol banidashi kuma ba mai bani, na zama abin kwatance a idon duniya, gani ga wane ya ishi wanne soron Allah, nayi nadaman duka karuwancinda nayi diga baya, da duka shashanci,  da barikanci, wannan ai shi ake cewa hisabi tun baka mutu ba, toh karku kuskura ku sawa yaranku suna munira, kuma inaso ku maidani abin kwatance ga yaranku da jikokai, ina cikin nadamar rayuwar danayi diga baya, Allah ka yafemin.”
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like