Da Ɗumi-Ɗuminsa: Rikici na neman kaurewa tsakanin Saudiyya da Amerika

Advertisements

Rahotannin da ke shigo mana yanzu sun tabbatar da cewa wani karamin rikici na neman kaurewa tsakanin Kasar Saudiyya da Amurka. Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne Kungiyar da ke da tattalin arzukin Man Fetur a fadin duniya, wato OPEC suka gudanar suka gudanar da taron yadda zasu rage yadda suke samar da man ferur a duniya.
Sai dai bayan wannan taron tattaunawar Shugaban Kasar Amurka ya ziyarci kasar Saudiyya don rokon kasar da su bashi wata daya kafin su fitar da sakamakon wannan zama.
Bayan sun amince, daga baya sai aka jiyo mukarraban kasar suna cewa babu abinda zai canza wannan sanarwar da zasu fitar. Sai dai hakan bai yiwa Shugaban Amurka Biden dadi ba, inda aka hango shi yana magana a gidan TV yana fadan cewa ba zai fadi abinda zai yiwa Saudiyya ba, Amma tabbas zasu ga sakamako.
Hakan ya sanya wasu daga cikin yan kasar Saudiyya suka fara mayarwa da Amurka martani, inda suke bidiyo suna saki a kafar sada zumunta. Shin kuna ganin Saudiyya zata iya karawa da Amurka kuwa? 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like