Advertisements
Duk wadanda suka sanshi sai dai su fadi alheri, nagarta da kuma kyawawan halayyarshi Wadanda suka karanta tarihinshi a natse, suna yawan yabawa tare da jinjinawa irin rayuwar da yayi a duniya.
Chicharito dan wasan kwallon kafa ne na kasar Mexico wanda ya bayyana Annabi a matsayin mutum mafi nagarta a duniya, duk da kuwa Kirista ne.
Wadanda Suka sanshi ko suka karanta wani abu a kan shi, sun san irin albarkatacciyar rayuwar da yayi. An gano cewa ‘yan kwallo da sanannu a duniya na nuna mishi soyayya saboda tarihin shi da suka samu.
Wanna ba kowa bane sai Annabi Muhammad SAW. An turo shi ne zuwa ga mutane baki daya. Ba Annabin musulmai bane kadai, dukkan mutane ne za a musu hisabi da zuwanshi.
Wani babban dan wasan kwallon kafa daga kasar Mexico, Javier Hernandez Balcazar wanda aka fi sani da ‘Chicharito’ ya shiga sahun masoya Annabi.
A daya daga cikin wallafar da yayi a shafinshi na tuwita, ya bayyana irin kaunar da yake wa manzon ta yadda ya ce shi ne mutum mafi nagarta a duk duniya.