Wata mata ta mayarwa mijinta kudin da ta tsinta a aljihunsa ya yin da ta yi masa wanki

Advertisements

Wata mata ta bayyana yadda ta mayarwa da mijinta kudin da ta tsinta a ya yin da take yi masa wanki, inda ya nuna jindadinsa a Lokacin da ya dawo gida ta bashi kudin.
Wani bidiyo ne aka samo a Manhajar tiktok na wata mata tana yiwa mijinta wanki har ta tsinci kudi a aljihunsa ya dawo ta durkusa ta bashi sai ya rungumeta
Shi ne wasu suke ce mata matar kirki wasu kuma suke cewa duk yadda suka auri matar kirki ba zasu sata wanki ba  wasu matan ma suke cewa suma ba za su yi wa mijinsu wanki ba wasu kuma suke ganin ai kyautatawa ce.
Ya yin da muka ci karo da ra’ayoyin mutane sun ga ra’ayin wani mai suna Farooq Abdullahi, kan yadda mata ke yiwa mazajensu wanki a gidajensu. Ya bayyana cewa
“Nidai gaskiya ba zan iya sa matata yi mun wanki ba gaskiya sai dai idan ita ce bana nan ta dauka ta wanke  don ni aciki abubuwan da suke wahalar dani shine wanki da guga tun dana fara neman kudi na daina yin su da kaina” Inji Shi
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like