Shekarun mu 14 da aure har yanzu ba a taɓa jimmu ba ni da Matata – Inji Lawan Ahmed

Advertisements

Fitaccen Jarumi kuma furodusa a masana’antar Kannywood, Lawan Ahmad ya bayyana cewa a zamansu da matarsa, Saratu Abdulsalam, babu wani ya taba kai karar wani tsawon shekaru 14 da aure.

Shafin Mujallar Film ta zanta da jarumin inda yace yana matukar farinciki tare da alfahari da cika shekaru 14 a ranar 25 ga watan Oktoban 2022, ba tare da an ji kansa da matarsa ba.

Advertisements

Ya wallafar zazzafan hotonsa tare da uwar ‘ya’yansa don murnar. Yayin tattaunawa da Mujallar Fim, jarumin ya ce:

“Alhamdulillah, ina farin ciki tare da alfahari da Allah cikin ikon sa yasa mu ka cika shekaru 14 da aure. Kuma babu wani a cikin mu da ya taba kai karar wani gidan iyayensa. Mu na zaune da dadi babu dadi, har mu ka cika shekarun nan.” Cewar Jarumin Kannywood Lawan Ahmed.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like