Advertisements
Kar a bari wani Munafukin Inyamuyi ya cire mana rubutun ajami a kudin Nijeriya – Cewar Sheikh Yahaya Jingir
Fitaccen Malamin Addinin Muslunci a Nijeriya da ke garin Jos jihar Filato, Sheikh Sani yahaya Jingir ya yi Kira ga Gwamnatin Shugaba Buhari da kada ta sake ta canza fasalin kudin Nijeriya.
Shehin Malamin ya yi wannan jawabi ne biyo bayan sanarwa da aka samu daga Babban Bankin Nijeriya wato CBN Kan canza fasalin kudin Nijeriya.
Sai dai Malamin ya ce “Kar ka bari wani Munafukin Inyamuyi ya taba mana rubutun ajami a kudin Nijeriya, Ni ban yadda ba, Inji Sheikh Jingir.