Bidiyo: Yadda mutanen gari suka tsige kan Dan ta’addan da ya addabesu a Katsina

Advertisements

Mutanen gari sun tsige kan wani dan bindiga a Batsari jihar Katsina. A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu Ƴan sa kai suna fafata da masu da ake zargin Yan bindiga ne a wani gari da ake Kira da Ruma, da ke karamar hukumar Batsari jihar Katsina.
Kamar yadda Jaridar Arewa take samun rahoto lamarin tare da bidiyon, ya tabbatar cewa barayin sun yi kokarin shiga garin ne, inda aka gansu da mashina tare da bindigogi. Sai dai wasu da ake kira yan sa kai sun tarbesu, inda suka yi arangama dasu.
Majiyar Jaridar Arewa ta tabbatar da cewa an ragargaji Ƴan bindigar, inda a cikin bidiyon an nuno yadda daya daga cikin mutanen gari ya riko kan wani ɗan ta’adda da ake zargin sun kawowa garin hari ne.
Sai dai har yanzu hukumar Ƴan sandan jihar Katsina bata fitar da faruwar lamarin ba. Wakilinmu ya bayyana mana cewa mutanen garin sun yi nasarar kwace mashinan Yan bindigar tare da kashe wasu da kuma jikkata wasu, inda ake sa ran wasu sun arce da gudu.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like