Advertisements
Shugaba Joe Biden na kasar Amurka Bayan wani gargadi kan yiwuwar samun hare-hare a Najeriya da Afirka ta Kudu, Gwamnatin Amurka ta yaba wa kasashen biyu kan abin da tace ingantuwar yanayi na tsaron.
Amurka ta yaba da kokarin da kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu ke yi a kan tsaro, bayan wani kashedin da ta yi na yiwuwar afka wa Abuja fadar gwamnatin Najeriya da hare-haren ta’addanci da ma wasu wurare da ke wajen birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.
A ranar Alhamis da ta gabata ne dai Amurkar ta yi kiran ma’aikatan jakadancinta da ke Abuja dasu fice daga Najeriya, kwana guda bayan ta yi hakan ga su ma ‘ya’yanta da ke a Afirka ta Kudu.
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu, ya nuna rashin jin dadi ganin yadda Amurkar ta yi gaban kanta wajen bayyana hadarin ba tare da ta tuntubi gwamnatin kasar ba.