Zan yi gyare-gyare a shafin Twitter bayan na mallaki Kamfanin _ Elon Musk

Advertisements

Sabon mamallakin kamfanin Tuwita Elon Musk ya ce za a sake duba hanyar da ake bi wajen tantance masu amfani da shafin.
Hakan na zuwa ne yayin da rahotonni ke cewa kamfanin zai fara cazar kwastomomin – da aka tantance shafinsu – dala 20 a wata.
Kwanaki bayan da ya sayi kamfanin Elon Musk ya wallafa a shafin nasa cewa za a sauya hanyar tantance masu amfani da shafin.
A halin yanzu dai tantance masu amfani da shafin – wanda ake saka wa shudiyar alama domin tabbatar da sahihancin shafin – kyauta ne.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai Mista Must ya kammala sayen kamfanin kan kudi dala biliyan 44.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like