Sanarwa mai mahimmanci dan gane da hatsarin da ke cikin Amfani da Manhajar VPN na Kyauta

Advertisements

Kwanan nan na ga maabota social media suna ta amfani da manhajar free VPN, wanda yake ba da dama a yi browsing kyauta, da yawan masu amfani da shi ba su san illarsa. Manhajar Free VPN, wani application ne da yake ba da damar yin dukkan nau’i na browsing a kyauta, amma yana da illoli matuƙa ga wayoyi da kuma rashin sirri ga mutum.
 Yin amfani da manhajar VPN na kyauta yana da matuƙar haɗari, zai iya janyo wa mutum abin da ko da wasa baya taɓa tunaninsa. Gara ma wanda ake biya kafin amfani da su ɗin, domin shi ɗin ana iya kare bayanan sirri na mai amfani da shi a kan kuɗin da bai taka kara ya karya ba.
Akwai mutane da dama waɗanda suke jin daɗin amfani da manhajar VPN na kyauta, to ya kamata tun wuri su sani cewa, amfani da VPN yana tattare da illoli, gasu a ƙasa za mu yi bayani ɗaya bayan ɗaya.
ZA A IYA SATAR BAYANANKA
Yawancin masu amfani da VPN ba su da masaniyar za a iya satar bayanansu cikin sauƙi. Ɗaya daga cikin muhimman dalilan amfani da manhajar VPN shi ne ganin an kare ka daga masu kutse, to amma fargabar ita ce maganar gaskiya wasu manhajojin na VPN na ƙunshe da wani siddabaru da ake amfani da shi wajen satar bayananka da kuma amfani da wannan dama wajen aiwatar da wata mummunar manufa da ake son cimmawa.
Irin waɗannan manhajoji na kyauta na VPN na amfani da tallukan da suke sanya wa masu amfani da su wajen wawashe bayanansu, kasancewar sun dogara ne da ‘yan tallukan da suke samu wajen samun kuɗin shiga.
BIBIYAR DUK ABIN DA KAKE YI
Wasu suna amfani da Manhajar VPN ne, saboda kare sirrinsu a lokacin da suke bincike a Internet ba, to sai dai yawancin manhajojin VPN na kyauta na da wasu mutane da aka sanya da ke bibiyar abubuwan da ke faruwa a cikinsu.
Suna tattara bayanan masu amfani da su, don haka a wannan bigire maimakon a aiko maka da wani tsari da kake da damar amincewa da shi ko ka latsa kalmar a’a, sai kawai a tunkuɗo maka talla, wanda a lokacin da kake kallonsa sai kuma a riƙa kwasar bayananka salin alin ba tare da ka danna komai ba.
TAƘAITA SAMUN BAYANAI
Yawancin VPN na kyauta na taƙaita adadin bayanan da za ka iya amfani da su. Suna yin wannan ne don tura masu amfani da su zuwa tsarin da ake biyan kuɗi kafin a samu cikakkiyar damar yin abin da ake son a yi, kamar yadda Hausawa ke cewa ”Iya kuɗinka iya shagalinka”
Manhajar VPN na haifar da damuwa ga masu amfani da ita saboda yadda take jinkirta sadarwar Internet (rashin sauri).
Manhajar VPN na kyauta na haifar da jinkiri wajen samun bayanai a Internet, abin da ke kawo damuwa ga wanda ke amfani da su, to dalilin shi ne yawancin mutane na raja’a ne ga na kyauta don cin bulus.
Sannan su kansu tallukan da suke sanya wa da zummar satar bayanai na iya haifar da rashin saurin na Internet, dalilin sanya tallan shi ne tun da masu amfani da su garaɓasa kawai suke ci, to bari su tallata wata haja tun da dama masu karin magana sun ce ”Da ruwan ciki ake jan na Rijiya”.
BARAZANAR HARBUWA DA CUTUTTUKAN INTANET 
Manhajojin da ake amfani da su wajen sadarwa a waya ko na’urar kwamfuta ko kuma Internet na ɗauke da wasu hanyoyi da yawa da ake sanya wa a cikinsu wajen satar bayanai ko yin kutse ko shirya wani siddabaru.
Wasu manhajojin na VPN da ake amfani da su a kyauta ana tsara su ne da zummar cewa masu su suna da ikon sarrafa bayanan mutane yadda suka ga dama, kuma suna ba da wannan ikon ga abokan cinikinsu masu biyan kuxi don riba.
Wannan yana da matuƙar haɗari kamar yadda ma su aikata laifuka ta yanar gizo ke iya yin amfani da wannan yanayin don ƙaddamar da hare-hare kan masu amfani da VPN da ba su da masaniyar duk wannan al’amari.
Manhajojin VPN na tattare da sarƙaƙiya iri iri da ke da buƙatar zuba kuɗi da yawa a harkar don samar da kariya da kuma tsare bayanan ma su amfani da su. Akwai kuma buƙatar masu su, su riƙa sabunta tsare tsaren ba da kariyar da suke amfani da su akai-akai daidai da zamani domin tabbatar da kare abokan hulɗarsu.
Sai dai kash, rashin mayar da hankali ga waɗannan abubuwa da suka kamata ne ya sa masu manhajar VPN ta kyauta ke cin karensu babu babbaka ta hanyar cusa talluka da wasu tsare-tsare da ke zama babban haxari ga masu amfani da manhajar.
A ƙashin gaskiya, wannan ba wai kawai abu ne mai matuƙar haɗari ba, ya kuma ci karo da dokokin bayar da kariya da tsaro da su kansu ƙa’idojin amfani da manhajojin na VPN.
Amfani da manhajar VPN zai zama ba ka da cikakkiyar kariya a dukkan mu’amalarka ta Intanet. Wasu ƙasashen tuni sun haramta amfani da manhajar VPN, saboda haɗarin dake tattare da ita. Dukkan sirrikanka suna hanun VPN muddin kana amfani da manhajar VPN. Sannan amfani da manhajar VPN yana zuƙar data fiye da na normal data.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like