YANZU-YANZU: Wani Ango ya rasu kwana daya da Aurensa a jihar Sokoto

Advertisements

Wani matashin ango mai suna Shehu Lili Kofar Atiku ya rigamu gidan gaskiya sa’o’i ashirin da hudu bayan an daura maaa aure a jihar Sokoto.

Wani abokin angon, mai suna Shamsudeen Buratai shine ya tabbatar da aukuwar lamarin. Buratai ya bayyana cewa Shehu Lili ya rasu bayan yayi fama da ‘yar gajeruwar rashin lafiya

Advertisements

A cewar Buratai, an daura auren angon ne a ranar Lahadi 5 ga watan Oktoba 2022, da misalin karfe biyar na yamma a unguwar Kofar Atiku sannan ya rasu da safiyar ranar Litinin.

“Shehu abokina ne tun na yarinta kuma dan’uwa na tsawon fiye da shekara 30. Yana fama da matsananciyar malaria wacce take taso masa duk lokacin sanyi. Kamar kowace shekara, ciwon nasa ya taso masa a bana a cikin watan Disamba, inda ya sha magunguna ya samu lafiya.” A cewar sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like