DA DUMINSA: Yan sanda sun kama wato Tunkiya sun kulleta bayan ta cinye wani soyayyen kifi a Borno

Advertisements

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno da ke Maiduguri ta cafke tare da tsare wata tunkiya ita kadai da ‘ya’yanta guda biyu sakamakon korafin da aka yi na cewa ta ci tulin soyayyen kifi da aka baje domin sayarwa.

Lamarin ya faru ne a unguwar Bulabulin da ke cikin karamar hukumar Maiduguri a ranar Asabar.

An ce har yanzu ana ci gaba da tsare tunkiya da ‘ya’yanta har zuwa yau safiyar Lahadi, an kama su ne biyo bayan wani korafi da wani mai suna Yusuf Ibrahim da ke sayar da kifin ya kai hedikwatar ‘yan sanda na Bulabulin da ke kan hanyar da ke cunkoso a unguwar.

Advertisements

A cewar Zagazola Makama, wani masani kan yaki da tada kayar baya kuma manazarci kan harkokin tsaro, Ibrahim ya koka da cewa tun shekaru da dama ne tunkiya ke ‘ ta’addanci da shi.

Jaridar Arewa ta ruwaito cewa ya ce ya daure da kutsen da dabbar ta aikata har na tsawon shekaru biyar, amma abin da ta yi a ranar Asabar ya jawo masa hasara mai yawa, Ibrahim ya kara da cewa tunkiya ta zama dabi’a ta zagaya shagonsa tare da yin hakuri daga nesa. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like