Advertisements
Wani bidiyo da ya bazama a kafafen Sadarwa na Zamana, musamman Manhajar Tiktok ya bayyana yadda wani dan kasar Saudiyya ke kokarin lalata da wata Yar asalin kasar Nijeriya da ke zama a cen.
Bidiyon Mai kimanin tsaron sakon 30, inda yake bayyana yadda wani balarabe ke kokarin lalata da wata budurwa Yar Nijeriya, ya yin da take yin girkin Abinci.
A cikin bidiyon an ga ya shigo kicin din, sannan ya kulle kofa, inda ya matso kusa da ita yana shafata, har ta kai ga yana kokarin fidda wandonsa domin yin lalata da ita. Da ta Ankara da hakan sai tunkude shi kamar yadda aka nuna a cikin bidiyon.
Rahotannin sun bayyana cewa yarinyar suna aikin dafa Abinci ne a kasar Saudiyyar, inda ake biyansu, sai dai wasu daga cikin bara gurbin yan kasar suna amfanin da wannan damar, don yin lalata da yayan mutane.
Abin ya jawo cece-kuce a kafafen Sadarwa, inda wasu suke Kira ga hukumomin Saudiyya da su gano wannan mutumin, sannan su dauki tsatstsauran mataki akansa, domin ya zama izina ga na gaba.