Jami’ar Fudma za ta fara aiwatar da Difiloma na karatun Al-kur’ani da bada Satifiket

Advertisements

Jami’ar Tarayya Dake Dutsinma A Jihar Katsina Za Ta Fara Karatun Difloma Da Satifiket Kan Alkur’ani Mai Girma
Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, FUDMA, da ke Jihar Katsina, ta ce nan ba da daɗe wa ba za ta fara gudanar da karatun Difloma satifiket da satifiket mai zurfi kan ilimin Alkur’ani.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Habibu Umar-Amin ya fitar a yau Laraba a Katsina.
A cewarsa, cibiyar nazarin kur’ani da bincike ta jami’ar, CQSR, ta kammala shirye-shiryen fara karatun.
Ya ce, Daraktan cibiyar, Dakta Jabir Musa Suleiman, ya ce shirye-shiryen sun hada da Difloma a kan ilimin.
Alkur’ani, babbar shedar karatun Alkur’ani da kuma kwas mai zurfi na shedar karatun Alkur’ani.
Ya nakalto Musa Suleiman na cewa tsawon shirin na difloma shekaru biyu ne, kuma ana bukatar mutum ya haddace Alkur’ani mai girma da sauran sharudda da a ke buƙata a cika sannan a nemi shiga fannin karatun.
Ya ci gaba da cewa: “Sharudda kamar yadda Musa-Suleiman ya ambata su ne maki hudu a sakamakon jarrabawar fita da ga sakandire, wadanda suka hada da Harshen Larabci da na ilimin addinin Musulunci.
“Lokacin yin satifiket ɗin kuma zangon karatu biyu ne, wanda ya ƙunshi azuzuwan daban-daban guda uku waɗanda suka haɗa da matakin farko da matakin gaba.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like