Tsakanin mu da Rarara Babu Sulhu, yanzu aka fara yancen – Inji Mustapha Naburiska

Advertisements

Mustapha Nabraska, mashawarci na musamman ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin farfaganda ya bayyana cewa su day Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara babu sulhu a tsakaninsu.
Ya bayyana haka ne a ya yin da gidan Jarodar DCL Hausa suka zanta da shi a ranar Talata, inda ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda Mawaƙin baya tafiyar Dan takarar Gwaman Jihar Kano a Jam’iyyar APC.
Naburiska ya bayyana cewa Ganduje ba zai taba rushe masa gida ba, saboda ba gidansa ba ne a gabansa, amman yana mamakin yadda Mawakin ya bujirewa tafiyar Gwamnan APC a jihar Kano, inda yanzu yake tafiyar Sha’aban Sharada. 
Naburiska yace tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Mawaƙi Rarara babu sulhu
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like